• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

JIBWIS-MU NA KIRA GA SAUDIYYA TA KARA YAWAN ALHAZAN HAJJIN BANA

Shugaban JIBWIS Sheikh Abdullahi Bala Lau ya yabawa hukumomin Saudiyya bisa bude dama don gudanar da aikin hajjin bana biyo bayan annobar korona da ta dakatar da zuwan alheri daga kasashen waje bara.

Malamin wanda ya lura da irin matakai masu inganci da Saudiyya ke dauka wajen yaki da cutar ta annoba don amfanin masu ibada a haramin Makkah da Madina; ya ce damar zuwan maniyyata dubu 45 cikin dubu 60 daga ketare gagarumar nasara ce in an duba yanda lamarin ya faru bara da takaitattun alhazai a cikin Saudiyya.

A nan Sheikh Bala Lau ya bukaci Saudiyya ta duba kara yawan kujerun ga kasashe irin Najeriya inda cutar ta annoba ba ta yi tsanani ba.

Malamin na ahlussunnah ya ce akwai gagarumar ribar zuwan maniyyata daga sassan duniya don taruwa a wajejen mafiya tsarki a yi addu’o’i na musamman na neman taimakon Allah ga yaye wannan annoba da ta addabi kasashen duniya.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.