• Fri. May 20th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

JANAR IRABOR YA TABBATAR DA MUTUWAR SHUGABAN DAESH NA AFURKA TA YAMMA AL-BARNAWI

ByNasiru Adamu El-hikaya

Oct 17, 2021

Babban hafsan rundunonin sojan Najeriya Janar Lucky Irabor ya ba da tabbacin mutuwar shugaban Daesh na Afurka ta yamma Abu Musab Al-Barnawi.
Irabor na magana ne a wani taron ma’abota sadarwa a fadar Aso Rock.
Babban hafsan ya ce hakika Al-Barnawi yam utu kuma haka ne ya mutu.
Ba da irin wannan tabbacin na da muhimmancin gaske ya fito daga jagororin tsaro don ya kawo karshen rade-radin rashin tabbas na irin wadannan labaru.
Hatta lokacin da shugaban Boko Haram Abubakar Shekau ya hallaka kan sa, sai da rundunar sojan Najeriya ta fito ta tabbatar da hakan.
Yanzu dai ya nuna fitattun shugabannin ta’addancin sun mutu amma dai har yanzu a na fuskantar barazana daga ‘yan ta’addan da su ka rage ba su yi saranda ba.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “JANAR IRABOR YA TABBATAR DA MUTUWAR SHUGABAN DAESH NA AFURKA TA YAMMA AL-BARNAWI”

Leave a Reply

Your email address will not be published.