Jam’iyyar adawa ta NNPP na kara samun magoya baya daga manyan jam’iyyu da ke sauya sheka su na shiga jam’iyyar.
NNPP da a baya karamar jam’iyya ce yanzu ta na neman zama ta uku mafi yawan magoya baya musamman a arewacin Najeriya.
Tsohon gwamnan Kano Rabi’u Musa Kwankwaso wanda shi ne jagoran jam’iyyar, na da muradin samun goyon baya daga wadanda ba su gamsu da tafiyar manyan jam’iyyu na APC da PDP ba.
Zuwa yanzu an samu fitattun ‘yan siyasa na neman shiga jam’iyyar ta NNPP don yin takara a zaben 2023.
Za a kara fahimtar alkiblar jam’yyun bayan zabukan fidda gwani da za su kammala zuwa karshen watan nan don mika sunayen ga hukumar zabe a makwan farko na watan gobe.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
I was pretty pleased to discover this great site. I need to to thank you for your time for this particularly fantastic read!! I definitely appreciated every part of it and I have you book marked to see new stuff on your blog