Jami’in banki Muhammad Danbarde ya samu tikitin takarar gwamnan jihar Gombe a jam’iyyar PDP.
Danbarde wanda a 2019 ya nemi takarar a APC amma ya zo na biyu, ya sauya sheka zuwa PDP inda a yanzu ya samu nasarar samun tikitin.
Danbarde ya yi nasara kan shugaban kamfanin wutar lantarki na Kano KEDCO Jamilu Isyaka Gwamna.
Wakilai 328 ne a ka tantance don zaben inda Danbarde ya samu kuri’a 160 yayin da Jamilu Gwamna ya samu kuri’a 119.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
Good job on the new site! Now go ahead and submit it to our free directory here https://bit.ly/submityoursite1000