• Mon. Jan 17th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

JAMI’AN TSARON SUDAN SUN KASHE KARIN MUTUM 3 MASU ZANGA-ZANGAR KIN JININ SOJA

ByNoblen

Jan 7, 2022 , ,

Jami’an tsaron Sudan sun kashe karin mutum 3 cikin masu zanga-zangar kin jinin mulkin soja a kasar bayan kawar da gwamnatin riko ta farar hula a Oktobar bara.
Masu zanga-zangar sun kara cijewa da matsin lambar ya sa Abdallah Hamdok ya sauka daga kujerar firaminista bayan sake dawo da shi bayan juyin mulkin.
Dan gwagwarmaya a Sudan Nazim Sirag ya ce jami’an sun kashe mutum daya yankin Bahri da ke babban birnin kasar Khartoum da kuma mutum biyu a birnin Oumdurman.
Har yanzu dubban mutane na gudanar da zanga-zangar a Khartoum inda su kan fuskanci harbor mu su hayaki mai sa kwalla da ma albarusai masu rai.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *