• Sun. Dec 5th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

JAMI’AN TSARON DSS SUN CAJI BIYU DAGA MUKARRABAN IGBOHO DA TA’ADDANCI

Jami’an tsaron farin kaya na Najeriya DSS sun caji biyu daga mukarraban dan rajin kafa kasar Yarbawa Sunday Igboho da laifin aikata ta’addanci.

Mutanen biyu su na daga cikin mutum 12 da jami’an su ka cafke a Ibadan babban birnin jihar Oyo.

DSS ta gurfanar da mutanen biyu a gaban babbar kotun taraiya da ke Abyja don amsa caji biyar da su ka danganci ta’addanci.

Mutanen sun hada da namiji daya Jamiu Oyetunji da mace daya mai suna Amudat Babatunde.

Cajin daya ne da ya shafi Amudat bai shafi Oyetunji ba wato amfani da shafin ta na Fesbuk wajen zuga tada fitina.

Mutanen an caje su da mallakar bindigogi da albarusai 1,500

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *