• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

JAMI’AN TSARO ZA SU YI DIRAR MIKIYA KAN MASU NIYYAR HARGITSA ZABEN ANAMBRA – MONGUNO

ByNasiru Adamu El-hikaya

Oct 27, 2021

Mai taimakawa shugaban Najeriya kan tsaro Manjo Janar Babagana Monguno mai ritaya ya gargadi masu barazana ga zaben gwamnan Anambra su sauya tunani don jami’an tsaro na shirye wajen dirar mikiya kan wanda ya nemi hargistsa zaben.

Ana shirin gudanar da zaben a ranar 6 ga watan gobe tsakanin manyan jam’iyyu da su ka hada da APC, PDP da AFGA da ke mulki a jihar.

Rahotanni na nuna ‘yan awaren Biyarafa/IPOB na shirya kawo fitina ga zaben da kuma hana shi yin nasara ta hanyar umurtar mutane kar su fito daga gida.

Monguno ya ba wa al’ummar Anambra tabbacin daukar dukkan matakai daga jami’an tsaro don gudanar da zaben lami lafiya.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.