• Sun. Dec 5th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

JAMI’AN TSARO SUN HALLAKA ‘YAN BINDIGA UKU A KADUNA

Jami’an tsaro a jihar Kaduna sun hallaka ‘yan bindiga uku a wata arangama a yankin Zangon Kataf.

Kwamishinan tsaro da lamuran cikin gida na jihar Samuel Aruwan ya baiyana haka a wata sanarwa.

Aruwan ya ce wani yaro mai shekaru 9 ya rasa ran sa inda wani mai shekaru 15 mai suna Faisal ya samu kunar wuta, hakanan an kona motoc 3 da gidaje 5.

Aruwan ya ce jami’an tsaron sun kalubalanci ‘yan bindigar inda su ka gama da uku daga cikin su yayin da wasu su ka arce daji da raunukan albarusai.

Jihar dai ta jinkirta dawowar dalibai makarantu a litinin din nan don illar ‘yan bindiga.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *