• Thu. Aug 18th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

JAMI’AN HUKUMAR ZABE NA KAURON MAGANA KAN MACHINA

ByNoblen

Jun 27, 2022

Jami’an hukumar zaben Najeriya INEC na kauron magana kan batun dan takarar majalisar dattawa na Yobe ta arewa a APC Bashir Machina.

Da alamun an bukaci jami’an su takaita magana kan batun kasancewar hankali da hakan ke ja na mutane su yi ta sharhi don ya shafi shugaban majalisar dattawa Ahmed Lawan.

Hakanan batun na da sarkakiya don sai an samu takardar a rubuce ta janyewa daga Machina kafin yin sauyin da jam’iyyar ke bukata, kuma Machina maimakon hakan ma ya garzaya kotu ne don ta tilastawa jam’iyyar ta mika sunan sa.

Kazalika hukumar ba za ta karbi sunan wand aba a gudanar da zaben fidda gwani da shi ba.

A gefe guda an hargitse da muhawara tsakanin magoya bayan Ahmed Lawan da Bashir Machina kan sahihin mai takarar.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “JAMI’AN HUKUMAR ZABE NA KAURON MAGANA KAN MACHINA”

Leave a Reply

Your email address will not be published.