Jama’a da dama a jamhuriyar Nijar na nuna farin ciki da yanda sojan saman kasar su ka yi ruwan wuta kan ‘yan ta’addan Boko Haram a yankin Diffa.
Lamarin ya burge mutane da a baya ba su dauka kasar na da jiragen yaki da za a iya amfani da su wajen tunkarar miyagun iri ba.
Wadanda a ka zanta da su na fatar irin wannan mataki ya dore don cin galaba kan ‘yan ta’addan da kan fito daga Najeriya su aukawa sassan jamhuriyar Nijar.
Yankin Diffa sha fama da hare-haren Boko Haram inda hakan kan jawo asarar rayuka.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀