• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

JAKADAN AMURKA A YAMAN LANDERKING YA NUNA KWARIN GUIWAR NASARAR TSAGAITA BUDE WUTA

ByNoblen

Sep 13, 2022

Jakadan Amurka a Yaman Thomothy landerking ya nuna kwarin guiwar tsagaita bude wuta tsakanin dakarun gwamnatin Yaman din da ‘yan tawayen houthi masu samun mara baya daga Iran.

Landerking ya baiyana cewa kungiyoyin shiyyoyin duniya sun mara baya ga daina yakin basasar Yaman ta hanyar hana maida hannun agogo baya daga yarjeniyar da a ke ciki yanzu da za ta kammala a daya ga watan gobe.

Wannan yarjeniya ita ce ta biyu da a ka cimma karkashin kulawar majalisar dinkin duniya ta sanya bakin jakadan ta hans Grungberg.

Landerkiing wanda ya ke magana a ziyarar karfafa diflomasiyyar sulhun a birnin Riyadh din Saudiyya, ya ce matukar ‘yan tawayen houthi su ka zabi cigaba da amfani da matakin soja a batun fitinar ta Yaman, to za a mayar da su saniyar ware.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.