• Fri. Jul 1st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

JA’AFAR JA’AFAR YA TAFI INGILA DON FARGABAR DA YA SHIGA

Babban editan jaridar yanar gizo ta Daily Nigerian Ja’afar Ja’afar ya arce zuwa Ingila don abun da ya zaiyana da kare rayuwar sa.

Ja’afar ya ce shi da iyalin sa sun yi hijira zuwa ketare har sai lamarin tsaro ya inganta kafin ya dawo.

Dan jaridar shi ne ya yi amfani da kafar labarun sa wajen yada faifan bidiyon da ke nuna cewa gwamna Abdullahi Umar Ganduje ne ke karbar toshiyar baki na dala.

Wannan lamari ya kai ga har majalisar dokokin Kano inda ta duba lamarin yayin da gwamnatin Kano ta yi watsi da faifan da baiyana cewa an cusa abubuwan da ba gaskiya ba a cikin sa don bata sunan gwamnan.

Ba mamaki fita ketare da Ja’afar ya yi na da nasaba da tuhumar da rundunar ‘yan sanda ke yi ma sa na bata sunan babban sufeton ‘yan sandan duk da ba a tantance sabon sufeto Usman Alkali a ke nufi ba ko tsohon sufeto Muhammad Adamu.

Irin yanayin salon ba da labari na Ja’afar ko a ce lamarin da ya shafi tone-tone kan jefa ‘yan jarida a rashin kwanciyar hankali.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.