• Sat. Nov 27th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

IYORCHIA AYU YA ZAMA DAN TAKARAR AREW NA SHUGABANCIN PDP

ByHassan Goma

Oct 17, 2021

Tsohon shugaban majalisar dattawa Iyorchia Ayu ya zama dan takarar shugabancin babbar jam’iyyar adawar Najeriya PDP daga arewa.
Dama jam’iyyar ta tura shugabancin jam’iyyar ga arewacin Najeriya.
Tsohon gwamnan Katsina Ibrahim Shema da Sanata Abdul Ningi sun janye daga takarar da hakan ya ba da dama Ayu daga jihar Binuwai ya zama dan takarar.
Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri ya sanar da sakamakon cankar Ayu a taron da masu ruwa da tsaki su ka gudanar a gidan gwamnatin Buachi da ke anguwar Asokoro a Abuja.
Za a gudanar da babban taron PDP a karshen watan nan na Oktoba inda za a zabi sabbin shugabannin jam’iyyar da za su tsara tunkarar APC a babban zaben 2023.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “IYORCHIA AYU YA ZAMA DAN TAKARAR AREW NA SHUGABANCIN PDP”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *