A cigaba da ragargaza Gaza don murkushe karfin Palasdinawa ‘yan Hamas, sojojin Israila sun sauke bom kan gini mai hawa 12 da hakan ya tada gagarumar kura.
Ginin ke dauke da ofisoshin jarida na duniya irin AP na Amurka da Aljazeera na Qatar.
Hakanan ginin na da gidajen kwanan jama’a.
Israila na son rufe kafofin labaru daga samun labarun abubuwan takaici da ke faruwa a hare-hare kan Gaza.
Sanadiyyar wannan hari kan kafafen labaru, shugaban Amurka Joe Biden ya yi magana da firaministan Israila Benjamin Netanyahu da shugaban Palasdinawa Mahmud Abbas.
A hari daya kadai da Israila ta kai kan wani sansanin ‘yan gudun hijira, Palasdinawa 10 su ka mutu da akasari yara ne kuma ‘yan uwan juna.
Hakanan a wani hari Israila ta yi amfani da jiragen yaki 160 da sauke boma-bomai masu nauyin ton 80.