• Thu. Aug 18th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

ISRAILA TA BUNNE YAHUDAWA MUTUM 45 DA SU KA MUTU

ByNoblen

May 1, 2021

Kasar Israila ta bunne mutum 45 da su ka mutu sanadiyyar tattake su da a ka yi a rububin ibadar Yahudawa da a ka dauka hakan na daga manyan bala’o’i da su ka taba kasar.

Lamarin ya auku ne a hubbaren daya daga manyan waliyyan Yahudawa Rabbu Shimon Yochai inda asalin masu bin addinin Yahudawa na dauri ke hutun da su ka yi wa taken Lag BaOmer.

Turmutsin ya auku ne da dare yayin da dafifin Yahudawa su ka taru a wannan bigiren don babban taron ibadar su.

Cikin kasashen Larabawa da su ka tura juyayin mutuwar mutanen da sarkin Jodan Abdullah.

Tuni shugaban Amurka Joe Biden da sarauniya Elizabeth su ka aika ta’aziyya.

Rahoto ya baiyana cewa an gargadi mutane kar su wuce dubu 10 a hubbaren amma dai da a ka samu mutum dubu 90.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “ISRAILA TA BUNNE YAHUDAWA MUTUM 45 DA SU KA MUTU”
  1. Hi there very nice blog!! Man .. Excellent ..

    Amazing .. I will bookmark your blog and take the
    feeds additionally? I’m satisfied to search out so many useful information right here within the put up,
    we need work out extra techniques on this regard, thank you for sharing.
    . . . . .

Leave a Reply

Your email address will not be published.