• Wed. May 25th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

IRAN TA ZARTAR DA HUKUNCIN KISA KAN DAN KOKAWAR ZAMANI NAVID AFKARI DA TUN FARKO A KA YANKEWA HUKUNCIN KISA

ByNasiru Adamu El-hikaya

Sep 13, 2020

Iran ta zartar da hukuncin kisa kan dan kokawar zamani Navid Afkari wanda a ka yankewa hukuncin kisa bisa zargin sa da kashe wani mutum mai suna Hassan Turkman a lokacin zanga-zangar kin jinin gwamnatin kasar da mutane ke zargi da jefa mutane cikin talauci ga kuma aukawa cin hanci da rashawa.

Babban alkalin yankin Fars Kazem Mousavi ya baiyana zartar da hukuncin kan Afkari a gidan yarin Adelabad a Shiraz.

Dubban mutane a 2018 sun gudanar da zanga-zanga inda jami’an tsaro su ka yi mu su rubdugu don karya lagon su.

Shugaba Donald Trump na Amurka tun farko ya bukaci hukumomin Iran su dakatar da kashe Afkari

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.