• Sat. Jul 2nd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

IRAN NA SHIRIN KASHE DAN KOKUWAR ZAMANI NA BIYU MEHDI ALI

‘Yan watanni bayan rataye dan kokuwar zamani Navid Afkari duk da sanya bakin kasashen duniya, kasar Iran na shirin rataye dan kokawa na biyu Ali Mehdi.

In za a tuna Iran ta rataye Afkari ne don zargin sanadiyyar mutuwar wani ma’aikacin ma’aikatar ruwa a zanga-zangar kin jinin gwamnati a 2018.

Shi kuma Ali Mehdi ya tsinci kan sa a hannun jami’ai bayan hatsaniyar da ta kai ga mutuwar wani mutum a 2015.

Iran na daga kasashen da kan yawaita zartar da hukuncin kisa kan lamura musamman da su ka shafi kin majalisar juyin kasar ta marigayi Ayatollah da ta faro a 1979 bayan tarzomar da ta kawo karshen mulkin Shah Reza Pahlavi.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.