• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

IRAKI: JAMI’AN TSARON SUN YI AMFANI DA RUWAN ZAFI DA BARKONON TSOHUWA KAN MASU ZANGA-ZANGA

Jami’an tsaro  a Iraki sun yi amfani da gwangwanayen ruwan zafi da borkonon tsohuwa kan dandazon masu zanga-zanga a Bagadaza da kudancin kasar da su ka fito don nuna kin jinin gwamnati.

Lamarin na zanga-zangar ya shafi cika shekara daya da kaddamar da gagarumar zanga-zangar ta kin jinin gwamnati da ya yi anadiyyar mutuwar fiye sa mutum 500.

Dandazon ‘yan Iraki na nuna bacin rai kan yanayin masu mulkin kasar da su ke zargi ‘yan jari hujja ne da ke tsunduma lamuran cin hanci da rashawa da rashin tausayin talakawa.

Firaministan kasar Mustafa Al-Kadhimi wanda ya hau kujera a watan mayu bayan fatattakar wanda ya gada da ‘yan zanga-zanga su ka yi, ya zaiyana kan sa a matsayin mai marawa masu zanga-zanga baya.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
4 thoughts on “IRAKI: JAMI’AN TSARON SUN YI AMFANI DA RUWAN ZAFI DA BARKONON TSOHUWA KAN MASU ZANGA-ZANGA”
  1. Hmm is anyone else encountering problems with the pictures on this blog loading?
    I’m trying to find out if its a problem on my end or if it’s
    the blog. Any feed-back would be greatly appreciated.

  2. I got this web page from my friend who told me regarding this website and now this time I am visiting this site and reading very informative articles or reviews at this place.

Leave a Reply

Your email address will not be published.