• Mon. Jan 17th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

IPOB TA YI BARAZANA GA RUNDUNAR EBUBE AGU

ByNoblen

Apr 14, 2021

Kungiyar ‘yan awaren Biafra ta Nnamdi Kanu ta yi barazana daukar mataki ga sabuwar rundunar tsaron ‘yan banga da gwamnonin kudu maso gabashin Najeriya su ka kafa.

IPOB ta yi barazanar daukar matakin kisa kan duk wanda ya shiga rundunar mai taken Ebube Agu da a ka kaddamar a Owerri.

IPOB da gwamnatin Najeriya ta haramta ta hanyar kotu, na cigaba da barazana ga tsaro da hadin kan Najeriya.

Kungiyar ta gargadi matasa kar su shiga sabuwar rundunar.

Matakin IPOB ba ya rasa nasaba da yanda gwamnonin su ka ce ba su amince da hare-hare kan cibiyoyin ‘yan sanda da ‘yan IPOB din su ka aiwatar ba kwanan nan.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *