Kungiyar ‘yan awaren IPOB mai son kafa kasar Biyafara ta amince da dakatar da matakin hana mutane yawo a yankin kudu maso gabashin Najeriya.
IPOB dai ta dau matakin hana mutane fita musamman a ranakun litinin don matsa lambar sake shugaban su Nnamdi Kanu da ke hannun jami’an DSS bisa fuskantar tuhumar cin amanar kasa.
Sarkin Anacha wato Igwe Nnameka Achebe ya baiyana haka da nuna kungiyar ta ba da umurnin ‘ya’yan ta su ajiye makaman hana mutane zirga-zirga.
Matakin na IPOB na kawo matsolin gaske ga ‘yan kasuwa da ma mutanen arewa da kan fito don sayar da hajar su a yankin.
iPOB ta haddasa mutuwar mutane da dama ciki har da jami’an tsaro.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
Definitely, what a great website and revealing posts, I will bookmark your blog.All the Best!