• Wed. Dec 1st, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

INDIYA TA HAURA MUTUM DUBU 400 NA MUTUWAR MASU KORONA

ByNoblen

Jul 4, 2021 , , , ,

Kasar Indiya ta samu yawan mutane da suka mutu a sanadiyyar cutar da a ka danganta da korona sama da dubu 400.

Wannan ba zai zama abun mamaki ba in an yi la’akari da yawan mutanen kasar.

Indiya dai na kara azamar yin rigakafin cutar da kan ba wa wadanda a ka yi wa kariya da kwarin guiwar cigaba da harkokin su ba fargaba mai yawa.

Indiya ta zama ta uku a kasashen da su ka haura mutuwar korona sama da dubu 400 bayan Amurka da Burazil.

Kazalika Indiya ta samu mutum miliyan 30 da su ka kamu da cutar inda Amurka ce kadau ta haura wannan yawa a duniya.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *