• Sun. Jan 16th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

INA SON WADANDA KE CIKIN FITINAR ‘YAN BINDIGA SU YI HAKURI MU NA DAUKAR MATAKAI-SHUGABA BUHARI

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci wadanda ke fama da hare-haren ‘yan bindiga su yi hakuri don gwamnati na daukar matakan magance kalubalen.
A sanarwa daga mai taimakawa shugaban kan labaru Garba Shehu, shugaban ya ce jami’an tsaro sun samu karin kayan aiki don murkushe barayin daji.
Muhammadu Buhari ya nuna juyayi kan hare-haren ‘yan bindiga kan kauyukan jihar Zamfara kwanan nan inda gomman mutane su ka rasa ran su.
Sanarwar ta nuna jami’an tsaro za su cigaba da bin sawun barayin da ta ce su na arcewa ne don neman tsira biyo bayan barin wuta daga sojoji.
Hakanan sanarwar ta nuna jami’ai na sane da yanda ‘yan bindigar ke azawa mutane haraji da gasa mu su aya a hannu, kuma lalle za a yi maganin su.
Shugaba Buhari da kan say a ambaci barayin dajin a matsayin ‘yan ta’adda da hakan ya nuna gwamnati za ta tinkare a matsayin ‘yan ta’adda.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “INA SON WADANDA KE CIKIN FITINAR ‘YAN BINDIGA SU YI HAKURI MU NA DAUKAR MATAKAI-SHUGABA BUHARI”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *