• Sun. Jan 16th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

INA SON A CIGABA DA AIKIN DAWO DA BURTALIN SHANU-SHUGABA BUHARI

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ya na bukatar a cigaba da aikin dawo da burtalin shanu kamar yanda su ke a jamhuriya ta farko bisa dokar gwamnati.
Shugaban ya ce duk ministocin da ya nada na aikin gona tun daga Audu Ogbe zuwa wannan minister na yanzu Mahmud Muhammad ya umurci su, su dauko taswirar burtalin don dawo da shi.
Burtalin dai da ya ratsa dukkan sassan Najeriya musamman dazukan arewa masu fadi ya samu kutsawar manoma da gine-ginen gidaje.
Tare burtali ya haddasa makiyaya arangama da manoma wani lokacin har a kan samu salwantar rayuka.
Yayin da akasarin gwamnonin arewa su ka amince da wannan tsari in ka debe gwamnan Binuwai, gwamnonin kudu sun hana tsarin kiwo a fili da bukatar lallae sai makiyayan sun mallaki gonakin kiwon shanu na zamani.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *