• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

INA NEMAN GAFARAR LABARIN DA NA CE YARA 10 A KA SACE A KATSINA ALHALI SUN KAI 344 – GARBA SHEHU

Mai taimkawa shugaban Najeriya kan labaru Garba Shehu ya nemi gafarar ‘yan Najeriya don labarin da ya bayar cewa dalibai 10 a ka sace a Katsina amma yanzu ga shi an wayi gari an ga su 344 ban da ma wadanda su ka arce don neman tsira.

Shehu ya ce ba ya fadi haka don rage kaifin gaskiyar labarin ko ma’ana neman shashantar da ba sace yaran ba ne, amma yanayin bayanai ne sa ke hannu da su ka sa ambata hakan.

Shehu a shafin sa na twitter ya ce ya damu da halin da yaran su ka shiga kuma ya na neman ahuwar ‘yan Najeriya don ba da labarin da ya zama ba daidai ba ne.

Garba Shehu ya nanata mubaya’ar sa ga Najeriya sa neman a nuna na sa fahimta kan wannan tuntuben harshe.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI馃榾馃榾馃榾
3,493 thoughts on “INA NEMAN GAFARAR LABARIN DA NA CE YARA 10 A KA SACE A KATSINA ALHALI SUN KAI 344 – GARBA SHEHU”