• Fri. Jul 1st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

INA KIRA A SAKO DALIBAN JAMI’AR GREENFIELD DA KE HANNUN BARAYI-SHUGABA BUHARI

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci a sako daliban jami’ar Greenfield da ke hannun barayin mutane karkashin madugun su Sani Jalingo da a ke taken “BALERI.”

Shugaban a sanarwa daga mai taimaka ma sa kan labaru Garba Shehu, ya ce gwamnatin za ta cigaba da daukar kwararan matakan kare lafiya da dukiyar al’umma.

Shugaban ya ce matakan za su sanya duk ‘yan Najeriya su rika tafiyar su lokacin da su ke bukata ba tare da fargabar komai ba.

Shugaba Buhari ya nuna farin cikin sako daliban kolejin gandun daji ta Afaka su 17 bayan shafe fiye da wata daya a hannun barayin.

Jihar Kaduna ta zama tungar satar mutane da neman kudin fansa.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.