• Mon. Jan 17th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

INA FARIN CIKI DA LADAR DALA MILIYAN 10 DON RUTSAWA DA AYYASH- BAHAA HARIRI

ByNoblen

Mar 31, 2021

Babban dan marigayi firaministan Lebanon Rafik Hariri wato Bahaa ya nuna farin ciki da yanda Amurka ta ware Dala miliyan 10 ga duk wanda ya samar da bayanan da za su kai ga rutsawa da wanda ya kashe mahaifin sa Salim Ayyash.
Bahaa wanda babban attajiri na Saudiyya da Lebanon, ya nuna gamsuwa da matakin na Amurka don hakan ya sa a kama Ayyash don ta fuskanci hukunci kamar yanda kotun majalisar dinkin duniya ta same shi da laifi a shari’ar da a ka gabatar a bayan idon sa.
Bahaa ya ce kowa ya yi amanna Ayyash dan kungiyar Hezbollah ne ta ‘yan shi’a da ta boye shi don ya gujewa hukunci.
Bayanai sun nuna Ayyash mai shekaru 57 na nan a boye a Lebanon kuma shugaban Hezbollah Hassan Nasrallah ya ki mika shi don fuskantar hukuncin kashe firaminista dan Ahlussunnah.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *