• Mon. Jan 17th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

IN ‘YAN APC SU YI SAKIYAR DA BA RUWA SAI SU SHA KASA A ZABEN 2023-SHUGABA BUHARI

ByNoblen

Jan 7, 2022

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi gyaran kayan ka ga ‘yan jam’iyyar sa ta APC cewa in sun ki hada kai za su iya shan kaye a zaben 2023/
Muhammadu Buhari wanda ya ke magana a zantawa ta musamman da gidan talabijin na kasa NTA, ya ce rashin hada kai ne da son zuciya ya sanya PDP ta sha kaye a zaben 2015 da hakan ya kamata a yanzu ya zama darasi ga ‘yan APC masu mulki.
Shugaban ya ce duk mai son samun mukamin jam’iyyar a babban taron ta, ya yi kamfen don sam ba wanda za a nada haka kawai.
Da ya ke amsa tambaya kan dalilan sa na kin sa hannu kan sabuwar dokar zabe ta ba da dama a yi ‘yar tinke a fidda gwanin jam’iyya, shugaban ya ce ya dau matsayar ba da dama ne duk jam’iyyu su zabi tsarin da su ke son amfani da shi cikin 3 da su ka hada da ‘yar tinke, yin zaben ta hanyar wakilai ko sasantawa.
Hakanan shugaban ya ce ba don zaben sa ta hanyar ‘yar tinke ya sa shi lashe zaben 2015, ya samu nasarar ce don hadin kan jam’iyyun adawa.
Game da wanda zai marawa baya a zaben 2023, shugaban ya ce zai boye sunan sa a zuciyar sa don in ya baiyana za a iya hallaka shi.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *