• Thu. May 19th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

IKIRARIN HOUTHI NA CEWA RUNDUNAR LARABAWA TA KAI HARI KAN GIDAN YARI A SAADA NEMAN FARAGANA NE

Rundunar Larabawa da ke yakin dawo da zababbiyar gwamnatin Yaman ta baiyana ikirarin ‘yan tawayen houthi da Iran ke marawa baya cewa rundunar ta kai hari kan gidan yari a Saada da neman farafagandar yaudarar mutane.
Houthi ta ce a makwan jiya rundunar ta kai hari kan gidan yarin Saada da hakan ya yi sanadiyyar mutuwar kimanin mutum 90 da raunata fiye da mutum 200.
Rundunar ta ce hare-haren ta sun biyo bayan yanda houthi ta matsa kaimi wajen harba makaman masu linzami kan Daular Larabawa da kuma Saudiyya.
Hakanan rundunar ta zargi houthi da amfani da wajajen farar hula don samun kariya daga hare-haren da su ke bisa ka’idar yaki.
Rundunar ta ce za ta fidda shaidun gaskiyar abun da lamarin ya faru don karyata abun da ‘yan tawayen houthi su ka yayata

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.