• Mon. May 23rd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

IGP: YA YI UMURNIN DIRAR MIKIYA KAN MASU FAKEWA DA ZANGA-ZANGA SU TABKA TA’ASA

Babban sufeton ‘yan sandan Najeriya Muhammadu Adamu ya umurci mataimakan sa AIGs da kwamishinonin ‘yan sanda su dau matakan dirar mikiya kan duk masu fakewa da zanga-zanga wajen tabka ta’annati a fadin Najeriya.

Muhammadu Adamu ya umurci jami’an na sa su yi amfani da duk wani mataki da ya ke kan doka wajen hana duk wani laifi ko neman karya doka.
A wannan bigiren, Adamu ya bukaci ‘yan kasa masu zaman lafiya kar su firgita daga matakan da za a dauka.

Matakin ya hada da ‘yan sanda za su mamaye wajajen da a ke ganin akwai yanayin karya doka don daukar matakan da su ka dace.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “IGP: YA YI UMURNIN DIRAR MIKIYA KAN MASU FAKEWA DA ZANGA-ZANGA SU TABKA TA’ASA”
  1. We are a group of volunteers and starting a brand new scheme in our community.
    Your site provided us with valuable information to work on. You have performed a formidable task and our whole community might be grateful to you.

Leave a Reply

Your email address will not be published.