Idanu na kan kungiyar ‘yan tawayen houthi a Yaman da Iran ke marawa baya don bin yarjejeniyar tsagaita bude wuta.
An samu karin wa’adin yarjejeniyar da wata biyu don bude sabuwar damar sulhu da kawo karshen yakin basasar kasar da ya faro tun shekara ta 2014.
Majalisar dinkin duniya ta bukaci houthi ta tabbatar da bude yankin Taiz da ta hana sukuni don fara tawayen.
Jakadan majalisar dinkin duniya a Yaman Hans Grunberg na fatar sabuwar yarjejeniyar za ta kawo sulhu mai dorewa a Yaman.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀