• Mon. Jan 17th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

IDAN NAJERIYA TA WARGAJE KANANAN KABILU SUN SHIGA UKU-OBASANJO

Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya ce matukar Najeriya ta wargaje, kananan kabilu sun shiga uku don za a murkushe su ne.

Obasanjo wanda ke karbar bakuncin wata kungiyar ‘yan kabilar Tiv daga jihar Binuwai da ta ziyarce shi a Abeokuta, ya ce sam ba alheri ba ne wargajewar Najeriya musamman ga kananan kabilu don yanzu yanda Najeriya ta ke a dunkule na ba su kariya daga murkushewa.

Obasanjo ya ce har dai Najeriya ta wargaje Yarbawa su ka rike gefen su, Igbo su ka rike na su, Hausa/Fulani su ka rike na su, kananan kabilu ba su da madafa sai fuskantar tafiyar ruwa da su.

Tsohon shugaban ya ce ba ya mara baya ga wargajewar kasa.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *