• Mon. May 23rd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

HUSHPUPPI-KOTUN AMURKA TA TSAIDA WATAN OKTOBA DON FARA SHARI’AR DAMFARA

Kotun Amurka a California ta dage sauraron shari’a dan damfarar nan Hushpuppi daga watan mayu zuwa watan Oktoba na bana don bukatar wasu daga wadanda a ke tuhuma.

Shari’ar dala miliayn 1.1 ta shafi DCP Abba Kyari wanda a ke zargi da hada kai da Hushpuppi wanda asalin sunan sa Ramon Abbas.

In za a tuna hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka FBI ta bukaci mika Kyari don yi ma sa shari’a kan zargin na hulda da dan damfarar wanda ya ke tsare a Amurka.

Wannan na faruwa daidai lokacin da ministan shari’a na Najeriya Abubakar Malami ya shigar da bukatar dama daga babbar kotun taraiya don mika Kyari ga Amurka.

Hakanan Kyari ya na cikin tuhumar hulda masu fataucin kwaya daga hukumar yaki da fataucin kwayar ta Najeriya NDLEA.

Zuwa yanzu dai za a jira hukuncin kotu ne kan mika Kyari ko kuwa a’a, wanda kuma duk laifukan biyu ya musanta aikatawa.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “HUSHPUPPI-KOTUN AMURKA TA TSAIDA WATAN OKTOBA DON FARA SHARI’AR DAMFARA”
  1. I like this web site very much, Its a really nice berth to read and obtain information. “…when you have eliminated the impossible, whatever remains, however improbable, must be the truth.” by Conan Doyle.

Leave a Reply

Your email address will not be published.