• Sat. Jul 2nd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

HUKUMAR ZABEN NAJERIYA INEC TA DAGE KARBAR SUNAYEN ‘YAN TAKARA DAGA 3 ZUWA 9 GA WATAN GOBE

Hukumar zaben Najeriya INEC ta aiyana dage lokacin karbar jerin sunayen ‘yan takarar jam’iyyu daga ranar 3 zuwa 9 ga watan gobe.

Duk da wasu daga jam’iyyun sun gudanar da zabukan fidda gwani na gwamnoni da ‘yan majalisa, hukumar ta ce matakin amsa kiran jam’iyyun ne.

Kwamishinan labaru da ilmantarwa na hukumar Festus Okoye ya ce matakin ya biyo bayan taro ne da majalisar hadin kan jam’iyyun da ta bukaci a kara lokaci don 3 ga wata ya sa jam’iyyun sun takura.

PDP dai ta riga ta fada gudanar da zaben fidda gwanin don kusan duk wakilan da za su yi zaben da ‘yan takarar sun iso Abuja.

Mataimakin shugaban jam’iyyar na arewa Ambasada Umar Iliya Damagun ya ce ba sa fargabar komai don kwarewar su a lamuran siyasa.

Da alamu APC ta yi amfani da damar karin lokaci da hukumar zabe ta yi, inda ta dage babban taron ta zuwa 6 da 7 ga watan gobe.

Jigon APC Sanata Abu Ibrahim ya ce yanda APC kan dage lokacin zaben fidda gwani, logar lashe zabe ne ko samun galabar kan sauran jam’iyyu.

Musamman a yankin arewa mai yawan kuri’a jam’iyyun biyu na APC da PDP ke daukar hankali, inda a yanzu a ka samu kari da jam’iyyar NNPP.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.