• Sat. Jul 2nd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

HUKUMAR ZABE TA AIYANA BIODUN OYEBANJI A MATSAYIN WANDA YA LASHE ZABEN GWAMNAN EKITI

ByNoblen

Jun 20, 2022

Hukumar zaben Najeriya INEC ta aiyana Biodun Oyebanji a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Ekiti da a ka gabatar a karshen makwan gobe jiya.

Oyebanji na APC ya samu kuri’u mafi rinjaye dubu 187 inda ya yi zarra kan Segun Oni na jam’iyyar SDP wanda ya zo na biyu da kuri’u dubu 82.

Dan takarar babbar jam’iyyar adawa ta PDP Bisi Kolawole ya zo na uku a zaben da kuri’u dubu 67.

Duk da an baiyana gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali amma akwai zargin sayen kuri’u da a ka yi da hakan ya nuna kudi sun yi tasiri a zaben.

Tuni shugaba Buhari ya taya Oyebanji murna da nuna hakan ya sa APC na kara tasiri.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
8 thoughts on “HUKUMAR ZABE TA AIYANA BIODUN OYEBANJI A MATSAYIN WANDA YA LASHE ZABEN GWAMNAN EKITI”

Leave a Reply

Your email address will not be published.