• Thu. Aug 18th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

HUKUMAR YANAYI TA SAUDIYYA TA YI GARGADIN SAMUN HADARI MAI GIRMA A SASSAN KASAR

Hukumar yanayi ta Saudiyya ta yi gargadi ga ‘yan kasar na samuwar gagarumin hadarin ruwan sama a sassan kasar da dama.
Gargadin ya fara ne daga alhamis din nan zuwa asabar.
Sanrawar ta baiyana za a samu ruwan sama a sassan da su ka hada da Riyadh, Makkah, Madina, Hail, Qassim, shiyyar gabashi, Al-Baha, Tabuk, kan iyakar arewaci, Asir da Aljawf.
Za a samu ruwa sosai har ma da ambaliya a jumma’a da asabar inda za a samu zubar dusar kankara a tsaunukan Tabuka.
Kakakin rundunar kare fararen hula na Saudiyya Laftanar Kanar Muhammad Al-Hammadi ya shawarci jama’a su gujewa dukkan sassan da a ka iya samun ambaliyar ruwa.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “HUKUMAR YANAYI TA SAUDIYYA TA YI GARGADIN SAMUN HADARI MAI GIRMA A SASSAN KASAR”
  1. My brother suggested I would possibly like this blog. He used to be entirely right.
    This publish truly made my day. You can not imagine just how a lot time I had spent for this info!
    Thanks!

Leave a Reply

Your email address will not be published.