• Tue. Oct 4th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

HUKUMAR YAKI DA RASHAWA TA JAMI’AN GWAMNATIN NAJERIYA TA GURFANAR DA SHUGABAN KARAMAR HUKUMA DON KARBAR NA GORO

ByNoblen

Nov 24, 2021

Hukumar yaki da rashawa tsakanin jami’an gwamnati a Najeriya ICPC ta gurfanar da shugaban karamar hukumar Gwagwalada a Abuja don zargin karbar na goron Naira miliyan 10 daga hannun wani dan kwangila.
ICPC ta gurfanar da shugaban karamar hukumar Adamu Danze gaban babbar kotun Abuja don tuhumar zamba cikin aminci.
Labarin dai ya nuna Danze ya karbi kudin daga dan kwangilar da ke gudanar da aiki a yankin karamar hukumar.
A cikin tuhuma 6 da ICPC ke yi wa Danze akwai saba ka’ida ta hanyar umurtar dan kwangilar mai suna Aremu Omotosho ya tura kudin Naira miliyan 10 ga lauyan da ya ke kula da shari’ar zaben sa a gaban kotun kula da karar zabe.
An dage karar zuwa 1 ga Maris na badi da ba da belin Danze kan Naira miliyan 20 da mai tsaya ma sa da zai zama mai mallakar gida a yankin Abuja ko mai mukamin mataimakin darakta.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
2 thoughts on “HUKUMAR YAKI DA RASHAWA TA JAMI’AN GWAMNATIN NAJERIYA TA GURFANAR DA SHUGABAN KARAMAR HUKUMA DON KARBAR NA GORO”

Leave a Reply

Your email address will not be published.