• Mon. Jan 17th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

HUKUMAR TARA KUDIN SHIGA YAKAMATA TA BINCIKI WASU KAMFANONI DA SU KA MALLAKI FILAYE BA BISA KA’IDA BA-MAI KWARMATO

Wani mai kwarmato a Abuja Sule Nasir ya bukaci hukumar tara kudin shiga FIRS ta yi tsayin daka kan binciken yanda a ka yi wasu kamfanoni da a ka yi wa rejista a dare daya su ka mallaki filaye da girman su ya kai kadada 50 a gundumar Karsana a Abuja ba tare da biyan haraji ba.

Mai kwarmaton wanda ya dau shekaru ya na bin batun filayen da hakan ya kai shi har ga ma’aikatar shari’a, ya ce dan tsohon wani minista ne a zamanin mulkin Jonathan da mukarraban sa, su ka samu filayen daga hukumar Abuja ta barauniyar hanya.

Sule Nasir ya nuna takaicin cewa tsarin nan na biyan la’adar kashi 5% na kwarmato da gwamnatin shugaba Buhari ta kirkiro ba shi da tasirin samun la’adar ko kare rayuwar masu kwarmaton.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *