• Mon. Jan 17th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

HUKUMAR ALHAZAN NAJERIYA TA NUNA KADUWA BISA RASUWAR DR. ASHIRU DAURA

Hukumar alhazan Najeriya ta nuna juyayi ainun bisa rasuwar tsohon daraktan yanar gizo na hukumar Dr.Ashiru Sani Daura.

Marigayin ya rasu ne bayan fama da jinya a asibitin Shika da ke Zaria.

A sanarwa daga jami’ar labarun hukumar Fatima Sanda Usara, NAHCON ta zaiyana marigayin da cewa mutum ne mai kwazon gaske da ya gudanar da rayuwa abar koyi.

Sanarwar ta ce an ba da labarin marigayin ya bar wasiyya mai ban juyayi inda ya ce sam kar a dau hoto a jana’izar sa, kar a taru fiye da kwana uku kazalika duk lamarin jana’izar a yi ta bisa koyarwar sunnan Manzon Allah mai tsira da aminci.

Yanzu haka a na cigaba da aika ta’aziyya musamman zuwa Daura mahaifar marigayin da yi ma sa addu’ar samun rahama.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *