Kungiyar ‘yan tawayen houthi da Iran ke marawa baya ta ta kai miyagun hare-hare cikin Saudiyya da makamai masu linzami.
Daya daga cikin makaman ya dira a kan cibiyar kamfanin fetur na Saudiyya wata ARAMCO a birnin Jiddah inda gobara ta kama bal-bal.
An ga hayaki a sararin samaniya a Jidda daga bigiren da a ka kai harin.
Kakakin rundunar larabawa ta dawo da zababbiyar gwamnatin Yaman, Burgediya Janar Turki Almaliki ya ce hare-haren na da muradin nakkasa aiyukan samar da makamashi mafi girma ne a duniya.
Almaliki ya ce harin bai shafi rayuka ko lamuran jama’a nay au da kullum ba a Jiddah.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
I am glad to be a visitor of this staring site! , regards for this rare information! .