• Sun. Nov 28th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

HOUTHI TA YI BIRIS DA TAKUNKUMIN AMURKA TA KARA BARAZANA

ByNoblen

May 25, 2021 , , ,

Kungiyar ‘yan tawayen houthi da Iran ke marawa baya ta yi biris da takunkumin da Amurka ta azawa manyan kwamandojin ta, ta na mai barazanar cigaba da hare-hare da cilla jirage marar sa matuka.

Babban shugaban houthi Ali Houthis ya ce za su kaddamar da hare-hare kan sashen da su ka kulla kawancen yaki da su da ke karkashin jagorancin Saudiyya.

Kazalika Houthis ya zaiyana jama’ar sa da cewa masu jihadi ne don haka ba sa tsoro.

Amurka dai ta aza takunkumi kan kwamandojin houthi biyu da ke jagorantar miyagun hare-hare kan garin Marib da cigaba da kai hare-haren waje da yankin duk da sun cije a waje daya ba sa nausawa gaba.

Ba mamaki Amurka ta aza takunkumin don tilastawa ‘yan tawayen na houthi ‘yan shi’a su shiga tattaunawa da jakadan sulhu na Amurkar.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *