• Mon. Jan 17th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

HOUTHI TA HARBA MAKAMAI MASU LINZAMI 4 KAN MARIB INDA MUTANE SU KA SAMU RAUNUKA

ByNoblen

Dec 6, 2021 ,

Kungiyar ‘yan tawayen houthi da Iran ke marawa baya a Yaman ta kai hari yankin Marib inda hakan ya raunata mutum 3.
Makaman sun sauka a filin jirgi, anguwa Rawdha da Al-Shareka inda hayaki mai kauri ya turnuka sassan da boma-boman su ka fada.
Bayan harba makaman, an kaure da harbe-harbe a wajen birnin mai dauke da miliyoyin mutane.
Marib dais hi ne birni daya tilo da ke hannun gwamnatin Yaman ta Abed Rabbo a arewacin kasar.
Ministan labarun Yaman Moammar Al-Eryani ya bukaci jakadan majalisar dinkin duniya da na Amurka a kasar su yi tir da wannan hari da kuma aiyana houthi a matsayin kungiyar ‘yan ta’adda.
 

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *