• Sun. Nov 28th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

HEZBOLLAH CUTAR SANKARA CE GA LEBANON-MAJALISAR DOKOKIN AMURKA

Majalisar dokokin Amurka ta ce kungiyar ‘yan shia ta Hezbollah cutar sankara ce ta kasar Lebanon.

Furucin ya fito ne daga bakin shugaban tawagar majalisar dokokin da ta ziyarci birnin Beirut karkashin jagorancin Sanata Chris Murphy.

Tawagar ta gana da shugaban Lebanon Michel Aoun ta na mai furta kalamai masu kaushi kan yanda kasar ta ke jan kafa wajen kafa sabuwar gwamnati.

Murphy ya zaiyana Hezbollah da cewa kungiyar ‘yan ta’adda ce da ke yaduwa a cikin kasar.

Duk da caccakar Hezbollah, Murphy ya ce Amurka ba za ta juyawa Lebanon baya ba, a daidai lokacin da ta ke cikin mummunan yanayin karayar tattalin arziki.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *