Mummunan hatsarin tankar man fetur shake da man a babban birnin Saliyo Wato Freetown ya yi sanadiyyar mutuwar akalla mutum 99.
Hatsarin ya faru ne a sanadiyyar taho mu gama na motoci.
Da zarar aukuwar hatsarin, mutane sun garzaya don dibar man fetur da ke malala sai tankar ta kama da wuta.
Hatsarin ya haddasa rauni ga fiye da mutum 100.
Neman kwasar fetur a motar da ta fadi duk da hatsarin hakan ba sabon abu ba ne kuma zai yi wuya hatsari ya auku ba tare da tashin babbar gobara ba.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀