• Sun. Jan 16th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

HATSARIN MOTA YA YI SANADIYYAR MUTUWAR MUTUM 8 A BAUCHI

ByNoblen

Dec 20, 2021 , ,

An samu wani mumunan hatsarin mota a jihar Bauchi da ya hada da mota kirar Vectra da wata tifa inda mutum 8 su ka rasa ran su.
Hatsarin ya auku a hanyar Dass zuwa Buachi inda motocin biyu su ka yi taho mu gama.
Shugaban hukumar hana aukuwar hatsura na jihar Buba Abdullahi ya tabbatarwa kamfanin dillancin labarun Najeriya aukuwar hatsarin.
An alakanta hatsarin da lodi da ya wuce kima da kuma gudun tsiya.
Mutum 8 da ke cikin motar ta Vectra sun riga mu gidan gaskiya inda direban tifar ce kadai ya tsira da ran sa.
Mutanen 8 sun hada da maza biyu da mata 6. An kai gawawwakin marigayan babban asibitin Dass.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *