• Sun. Nov 28th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

HATSARIN JIRGIN ATTAHIRU-HUKUMAR BINCIKEN HATSARI TA MIKA RAHOTO

Hukumar bincike kan hatsari ta Najeriya AIB ta mika rahoton binciken abubuwan da a ka gano sun yi sanadiyyar hatsarin jirgin saman da ke dauko da tsohon babban hafsan sojan kasa Laftanar Janar Ibrahim Attahiru da da tawagar sa.

In za a tuna hatsarin ya auku a wajajen filin saukar jiragen sama na Kaduna inda Janar Attahiru da tawagar sa ta mutum 10 ciki har da akalla janarori 5 su ka rasa ran su.

Shugaban hukumar binciken hatsarin Akin Olateru ta mika rahoton ga babban hafsan sojan sama Isyaka Amao.

Ba a dai baiyana sakamakon binciken ba a rahoton mai sassa uku da gano dalilan hatsarin 27; ya  hada da shawarwari 8 da a ka bayar don aiwatar da su nan take.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *