• Wed. May 25th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

HASSAN NASIHA YA ZAMA SABON MATAIMAKIN GWAMNAN JIHAR ZAMFARA

Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ya zabi Sanata Hassan Nasiha Gusau ya zama mataimakin sa bayan tsige tsohon mataimakin gwamna Mahdi Ali.
Majalisar dokokin jihar ta tabbatar da tantance Hassan Gusau da a yanzu haka yak e matsayin dan majalisar dattawa daga Zamfara ta tsakiya a matsayin mataimakin gwamna.
Nasiha Gusau na daga ‘yan PDP da su ka samu zuwa majalisar dattawa bayan ture nasarar dukkan zababbu na APC a zaben 2019 da kotun koli ta yi bisa samun su da laifin rashin gudanar da zaben fidda gwani yanda ya dace.
Sakataren labarum PDP a Zamfara Umar Ahmed Shatiman Rijiya ya ce sun a kalubalantar tsige Mahdi a gaban babbar kotun taraiya da za ta fara sauraron karar ranar 10 ga watan gobe.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
2 thoughts on “HASSAN NASIHA YA ZAMA SABON MATAIMAKIN GWAMNAN JIHAR ZAMFARA”
  1. When someone writes an post he/she retains the idea of
    a user in his/her mind that how a user can be aware
    of it. Thus that’s why this article is amazing.
    Thanks!

  2. If you desire to grow your know-how just keep visiting this site and be updated with the hottest gossip posted here.

Leave a Reply

Your email address will not be published.