• Tue. Nov 30th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

HARIRI YA MIKA JERIN SUNAYEN MUTUM 24 DA YA KE SON AIKI DA SU A GWAMNATIN LEBANON

Firaministan mai niyyar hawa gado na Lebanon Sa’ad Hariri ya mika jerin sunan mutum 24 da ya ke son aiki da su a matsayin ministocin gwamnatin sa.

Hariri ya mika sunayen ga shugaban kasar Michel Aoun a fadar gwamnati a Beirut.

Hariri na cewa matukar a ka amince da sabuwar gwamnatin to za ta iya fitar da kasar daga mummunar halin da ta ke ciki na karayar tattalin arziki.

Sa’ad Hariri ya ce ya ba da dama zuwa alhamis din nan Aoun ya amince da gwamnatin ko in an samu akasi ya yi murabus.

Jerin sunayen na dauke da sabbin fuskoki.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *