• Mon. Jul 4th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

HARIN SATUMBA 2011 YA FI KARFIN MAFI MUNIN MAFARKIN MU-MARIGAYI KOFI ANNAN

Yayin da a ke bitar cika shekaru 20 bana da harin ta’addanci na shekara ta 2011 a cibiyar kasuwanci ta duniya a New York, hakanan a ke tuna martanin manyan jagororin cibiyoyin duniya irin tsohon babban sakataren majalisar dinkin duniya marigayi Kofi Annan.

Marigayin ya zaiyana harin da jiragen sama da cewa ya fi karfin yiwuwa ko da a mafi munin mafarki ne.

Da ya ke jawabi a zauren majalisar dinkin duniya Mr. Annan ya ce kasar da ta ke daukar bakuncin majalisar dinkin duniya wato Amurka da kuma birnin New York inda helkwatar majalisar ta ke fiye da shekaru 50, sun shiga yanayin hari daga ‘yan ta’adda.

Annan ya ce ba za a iya tunanin aukuwar hakan ba ko da a mafi munin mafarki ne.

Marigayin ya ce sun yi ta azamar neman kalmomin da su ka dace don tir da maharan amma ba su samu ba.

Kamar yanda a ka sani bayan harin,  Amurka ta dau tsauraran matakan yaki da abun da ta baiyana da ‘yan ta’adda musamman na kungiyar Alka’ida karkashin Osama Bin Laden.

Duk hare-hare kan duwatsun Tora Bora a Afghanistan don farautar Bin Laden ne amma sai a mulkin tsohon shugaban Amurka Barack Obama Amurka ta aiyana samun galaba a kan Osama.

A cika shekaru 20 bana daga kai harin, Amurka ta janye dakarun ta daga Afghanistan da hakan ya sa a ka tambayi masanin siyasar duniya na jami’ar Bayero Dr.Sa’idu Ahmed Dukawa, shin Amurka ta cimma dukkan muradun ta ne ko da sauran rina a kaba?.

Dr.Dukawa ya ce ko ba a bar baya da kura ba, amma ficewar ta Amurka ta fi zama da a’ala a yakin da ba shi da riba.

Harin dai ya shiga kundin tarihin duniya da kurewa masu sharhi tayar bayanai, amma ko duniya ta hakura wajen jingine batun a kundin tarihi duk da dubban mutanen da su ka galabaita a sassan duniya, hakika annobar korona ta nuna fin karfin soja wajen sauya tattalin arziki da alkiblar duniya.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “HARIN SATUMBA 2011 YA FI KARFIN MAFI MUNIN MAFARKIN MU-MARIGAYI KOFI ANNAN”
  1. I have read so many articles on the topic of the blogger lovers but this piece of writing is really a pleasant piece of writing, keep it up.

Leave a Reply

Your email address will not be published.