• Thu. Aug 18th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

HARIN ROKOKI YA YI SANADIYYAR RAUNATA KIMANIN MUTUM 3 A BIRNIN BAGADAZA

Wani harin da a ka kai da rokoki a babban birnin Iraki wato Bagadaza ya yi sanadiyyar samun raunuka ga kimanin mutum 3.
Harin dai ya fada gas ashen mafi tsaro a Bagadaza da a ke kira “GREEN ZONE” da ke dauke da ofisoshin jakadanci da zama masaukin jami’an diflomasiyya.
Rokokin sun fada harabar ofishin jakadancin Amurka da kuma wata makaranta da ke yankin.
Wata mata da yara biyu mace da namiji a harabar makarantar sun samu raunuka.
Ofishin jakadancin Amurka ya ba da tabbacin kawo harin amma hakan bai raunata kowa ba, kuma ya dace na’urar lalata roka ta ragarza rokokin.
Ofishin ya nuna masu harin na barazana ga tsaron Iraki da kuma lamuran diflomasiyya..
Iraki dai ta kasa zama lafiya duk da tunanin marigayi shugaba Saddam Hussein ne ke hana ruwa gudu, amma ga shi yau ba ya duniya amma sai hare-hare a ke ta kai wa a sassan kasar musamman birnin Bagadaza da Basrah.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
2 thoughts on “HARIN ROKOKI YA YI SANADIYYAR RAUNATA KIMANIN MUTUM 3 A BIRNIN BAGADAZA”

Leave a Reply

Your email address will not be published.