Harin jirgi marar matuki a Abu Dhabi, Daular Larabawa ya yi sanadiyyar mutuwar mutum uku da su ka hada da dan Pakistan daya da Indiyawa biyu.
Harin ya fada kan tankunan mai da hakan ya tada gobara har a ka samu asarar rayukan da kuma samun rauni ga wasu mutane.
Daga bisani kungiyar ‘yan tawayen houthi ta ‘yan shi’a a Yaman da Iran ke marawa baya ta baiyana daukar alhakin harin da cewa ita ta kai hari Abu Dhabi.
Daular Larabawa na daga kasashen da ke rundunar hadin guiwar larabawa da ke yakar ‘yan houthi a Yaman don karfafa zababbiyar gwamnatin kasar ta Abed Rabbo da ke aiki daga birnin Aden.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀